Tsohon dogarin Buhari ya nemi a tsige Monguno, Kyari da shugabannin tsaro

Rahotun Legit Hausa

Tsohon sarkin Gwandu, Manjo Mustapha Jokolo mai ritaya, ya nuna bakin ciki kan rikicin fadar shugaban kasa tsakanin mai ba shugaban kasa shawara a harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno da shugaban ma’aikata Abba Kyari.

Jakolo wanda ya kasance dogarin shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin da ya ke shugabanci a mulkin soja, ya yi kira ga Shugaban kasar a kan ya tsige su. Manjo Jakolo ya kuma bukaci shugaba Buhari da ya saurari muryoyin yan Najeriya sannan ya tsige shugabannin tsaro.

Basaraken wanda ya yi magana a wani shirin gidan radiyo a Kaduna ya bayyana cewa ba a taba samun sabani a tsakanin manyan jami’an gwamnati ba a lokacin mulkin soja saboda suna mutunta mukamin kowa da gudun shiga sharo ba shanu.

Ya ce, har sai dai idan shugaban kasa, Shugaban tsaro da shugaban ma’aikatan shugaban kasa sun bi tsarin al’umman Najeriya, idan ba haka ba sai Allah na kallonsu saboda Najeriya ta fi karfin kowani mutum.

Kan shugabannin tsaro, ya ce yan Najeriya basu ji dadin shugabannin tsaron ba sannan cewa kamata ya yi a tsige su sannan a sauya su da wasu da suka fi su. A baya mun samu labari cewa an samu sabani tsakanin wasu Jiga-jigai a gwamnatin Buhari, inda NSA Babagana Monguno ya ke zargin Abba Kyari da yin ba-ba-kere a fadar shugaban kasa.

Janar Babagana Monguno mai ritaya ya na zargin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, da shiga tsakanin wasu Jami’an gwamnati da shugaban kasa Muhammadu Buhari. Jaridar Premium Times ce ta fitar da wannan rahoto na musamman a Ranar Litinin, 17 ga Watan Fubrairun 2020. Abin har ta kai Babagana Monguno ya nemi a daina sauraron Abba Kyari.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN