Wata
Mata a garin Taquatinga na kasar Brazil ta kai karan wani mutum a Kotu
domin a cewar ta ,ta biya shi wasu kudade masu yawa wanda ba'a fadi ko
nawa bane domin ya kashe ta amma shi Mutumin wanda shi ma ba'a fadi
sunan sa ba ya kasa cika alkawarin kwantiragin da matar ta ba shi domin
ya kashe ta.
Ita dai wannan Macen,bayanai sun nuna cewa
ta yi fama da cutar matsanancin damuwa (depression) kuma tayi yunkuri
domin ta halaka kan ta a lokuttan baya amma ba tare da ta sami nassara
ba.Wannan dalilin ne ya sa ta dau hayan wani mutum mai kashe mutane kuma
ta biya shi domin ya kashe ta, bayan ta bashi makuddan kudi ta kuma ba
shi motar ta .Amma mutumin bai kashe ta ba wanda yin hakan ya harzuka
matar ita kuma ta garzaya zuwa kotu.
Bayan matar ta
shigar da kara a kotun garin Taquatinga,Alkalin Kotun ya baiyana mata
cewa tun asali ita wannan kwangila haramtacciya ce kuma baya cikin
tsari.Daga karshe dai Alkalin Kotun ya kori karar da Matar ta shigar a
gaban wannan Kotun.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari