Harin Chibok: Soja ya rasa kafarsa, an nemi biyu an rasa yayin da bam ya tashi da su

Rahotun Legit Hausa
Wani jarumin jami’in soja ya rasa kafarsa yayinda aka nemi abokan aikinsa biyu aka rasa yayinda suka taka Bam da wasu yan Boko Haram suka dasa a Korongilum, wani gari dake karamar hukumar Chibok, jihar Borno, TheCable ta ruwaito.

An tura Sojoji garin ne da safiyar ranar Laraba domin kawar da yan Boko Haram da suka garin daren Talata. Majiyoyi daga gidan Soja sun bayyanawa manema labarai ranar Alhamis cewa rundunar 117 Bataliya dake Chibok sun kusa isa garin Korongilum yayinda Bam ya tashi da motocin da suka dauke da su.

 “Sojoji bakwai sunyi matukar jikkata, kuma daya daga cikinsu ya rasa kafarsa“ “Kwamandan bataliyan, Laftanan Kanar SA Yahaya ne ya jagoranci tawagar. Da alamun shi aka nufa da Bam din amma ba ya cikin motar lokacin.“ cewar majiya Wata majiyar daban ta bayyana cewa “Da alamun yan taaddan Boko Haram sun dasa bama-bamai ne a wurare da dama cikin garin, kuma mutan garin na guduwa daga muhallansu.

“ Daya daga cikin mazauna garin ya bayyana cewa: “A yanzu haka, babu Sojoji a nan. Wadanda aka turo sun gamu da Bam jiya, har yanzu ba“a turo wasu ba“ Mun kawo muku rahoton cewa Yan taa’ddan Boko Haram na kan kai hari yanzu a garin Korongilum dake karamar hukumar Chibok ta jihar Borno.

Wani mazaunin garin ya bayyanawa manema labarai cewa yan ta’addan sun shiga garin ne misalin karfe 6 na yamma kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi. Hakazalika suna bankawa gidajen mutane wuta. Yace “Dawowar mutane gida daga gonakinke da wuya, sai yan taaddan suka shigo. Sun samu shiga ne ta Forfor, kuma mutane na guduwa yanzu.“

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN