Tap di jan: An kama wata mata da ta auri maza biyu a Kano, karanta abin da ya faru

Rahotun Legit Hausa

Wata matar aure mai suna Hauwa Kulu, mazauniyar unguwar Mariri a Kano, ta shiga hannun hukumar Hisbah, bayan an kama ta da laifin auren maza biyu a lokaci daya.

Da farko dai matar na zaune da mijinta na farko ne amma sai ciwo ya kama shi. Ita kuwa ta mayar da shi kauye inda aka ci gaba da jinyarsa. Bayan dawowarta ta ci gaba da zamanta, sai ta hadu da wani mutum wanda ta sanar da shi cewa ita bazawara ce. Bayan wani lokaci kuwa ya fitar da kudin sadaki aka daura musu aure.

Da yake direbane mijin na biyu, ya kan je nema sannan ya dawo wajen amarya a yi ta soyayya. Bayan dawowa daga wata tafiya ne suna daki tare sai ga mijin farko ya bayyana tare da kurma ihun cewa kwarto ya shigo masa dakin mata.

Shi kuwa mijin na biyu sai tashi yayi tare da fara tuhumar mijin cewa ya shigo masa gida har daki babu izini. A nan kuwa rikici ya balle wanda har ya kai su ga ofishin Hisba da ke yankin karamar hukumar Kumbotso.

A bangaren Hauwa Kulu kuwa mai auren maza biyu, ta bayyana cewa mijinta na farko Malam Bello ya sauwake mata, lamarin da Malam Bello ya musanta. Malam Bala kuwa, wato mijin Hauwa Kulu na biyu ya ce shi kuwa matarsa ce kuma babu wanda zai raba shi da ita. A halin yanzu ma kuwa suna da yaro daya namiji bayan ya tarar da ita da yara shida na Malam Bello

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN