Magidanci mai yara 4 ya mutun wajen dambe da wani mutum mai yara 5 domin masoyiya

Wani magidanci mai suna Mr Dickson Igbinoba mai shekara 42 ya mutu yayin da suke fada tare da wani mutum mai suna Mr Osakioya Egavoen mai shekar 41wanda suke jayayya tare akan wata mata. Mr Dickeson ya mutu ne bayan sun sha kulli daga junansu saboda wannan mata. Lamarin ya faru ne a shiyar Obasuyi rukunin gidaje na Egor da ke karamar hukumar Egor a jihar Edo.

Wannan lamari ya ba mazauna unguwar matukar mamaki ganin cewa mamacin watau Mr Dickson Igbinoba yana da aure har da yara hudu, shi kuma abokin hamayyarsa a kan wannan mata watau Mr Osakioya Egavoen shi ma yana da aure har da yara biyar, ita kuma matar da aka yi fada a kanta mai suna Ms Osasogie Edo-Ekhator mai shekara 37 ita ma tana da yara hudu.

Majiyar isyaku.com ta ce, rigimar ta faru ne bayan Mr Dickson wanda ke hutawa a cikin dakin Ms Osasogie ya dauki wayarta bayan ya ji wayar tana kara, amma bayan ya dau kiran wayar sai wanda ya kira watau Mr. Osakioya Egavoen ya ji muryar namiji a wayar Ms Osasogie, nan take sai ya tuka motarsa cikin fushi ya iso gidanta inda ya sami Mr Dickson kwance a dakinta yana hutawa.

Nan take cacan baki ya shiga tsakaninsu, lamari da ya kai ga zare damutsa, amma fa Mr. Dickoson ya kasa, sai ya yanke jiki ya fadi, daga bisani ya mutu. Ganin haka ke da wuya sai fada ya kare, shi kuma Mr. Osakioya Egavoen da ya yi kisa ta hanyar duka, sai ya ruga da gudu ya fice daga dakin Ms Osasogie, kuma ya yi batan dabo.

Amma Kakakin 'yansanda na jihar Edo DSP Chidi Nwabuzor ya ce 'yansanda sun kama Ms Osasogie tare da saurayinta mai kullin kisa Mr Osakioya Egavoen, ya ce yanzu haka masoyan sun riga sun ba 'yansanda jawabinsu kuma ana ci gaba da bincike a kan lamarin.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN