Rashin sauke manyan jami'an tsaro: Za mu kai Buhari kara a Kotu - Inji Falana

Fitaccen Lauya Femi Falana, ya bayyana aniyarsa ta gurfanar da shugaba Muhamadu Buhari a gaban Kotu, sakamakon rashin sallamar manyan jami'an tsaron Najeriya duk da kiraye kiraye da jama'a ke yi a kan lamarin.

Falana ya furta wadannan kalamai ne lokacin da yake tattaunawa da gidan Talabijin na Channels, ya ce "Shugabannin tsaron sun zarce shekara 35 na aiki kamar yadda doka ta shata".

A tattaunawar, Falana ya kara da cewa " Karkashin dokokin aikin Najeriya, kuma karkashin dokokin aikin sojin Najeriya, sashe na 6 na dokokin aikin soji, an ba shugaban kasa dama ya yi dokoki, amma ba inda dokar ta ba shi dama ya tsawaita wa'adin aikin shugabannin tsaro fiye da lokaci da doka ta kayyade".

" Can baya an yi haka, amma wannan ba hujja bane. Dole kowa ya kasance daidai da kowa a fuskar doka, ba adalci bane ka ce ma wasu su ajiye aiki domin sun cika shekara 35 suna aiki, lokaci daya kuma ka kara wa'adin aiki ga wasu, bayan sun zarce shekara 35 suna aiki, ko sun cika wa'adin shekara 60 da haihuwa".



" Na san za a shigar da kara a kan wannan lamari" inji Falana.


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN