Rahotun Legit Hausa
Mai shari'a Ahmed Tijjani Badamasi na babba kotun jihar Kano yayi watsi da karar masu hannu a nada sarki wacce ke kalubalantar kirkirar sabbin masarautu da kuma zabar sarakunan masu daraja ta farko.
Kamar yadda jaridar Solacebase ta ruwaito, masu hannu a nadin sabon sarkin sun maka Madakin Kano, Hakimin Dawakintofa, Yusuf Nabahani; Makaman Kano, Hakimin Wudil, Abdullahi Sarki-Ibrahim; Sarkin Dawaki Mai Tuta, Hakimin Gabasawa, Bello Abubakar da kuma Sarkin Ban Kano, Hakimin Dambatta, Mukhtar Adnan a gaban kotu.
Wadanda ake karar sun hada da gwamnatin jihar Kano, Gwamnan jihar, Kakakin majalisar jihar Kano da kuma kwamishinan shari'ar jihar Kano. Akwai Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero; Sarkin Karaye, Alhaji Ibrahim Abubakar; Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar da kuma Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir.
A yayin da aka koma sauraron kara a ranar Litinin, Mai shari'a Ahmed Tijjani Badamosi ya soke hukuncin Mai shari'a Usaman Na'aba wanda ya soke kirkirar sabbin masarautun a ranar 21 ga watan Nuwamba.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari