Type Here to Get Search Results !

Munanan illolin tsaka a gidan ka

Ga kadan daga cikin munanan illoli da ke tattare da tsaka.

1. Idan aka bar kowane irin garin abinci a bude, ta kan shiga tayi birgima a cikin garin. Bayan an tuka wannan garin, yawanci an kamu da cutan barasu wato kuturta ko wasu mugayen kuraje

2. Idan aka bar ruwan sha a bude sai tayi amai a cikin ruwan bayan ta sha ruwan. Yawanci sai ka ga an kamu da shanyewan jiki wato paralyze ko kuma lallacewar sassan jiki.

3. Idan mutum ya kwanta bacci bai yi addu’a ba, ta kanyi busa a cikin idon mutum. sai ka ga yawanci an samu lalacewar gani mai kyau ko a makance.

4. Idan tsaka ta rika, misalin ire-iren gobara da ta ke faruwa a yanzu so da dama tsaka ce amma bamu sani ba, domin ita tsaka tana tare da mugayen jinnu. Dama Fiyayyen Halitta Ya ce, ita ce tayi busa ga wutan da aka jefa Annabi Ibrahim (A.S).

5. An ta samu labarin wata mata da ta tafasa ruwan shayi da tsaka a cikin butan shayin, a sanadiyar wannnan tsakar ita da mijin ta, da yaran suduk suka bakunci lahira.

Kadan kenan daga cikin illolin tsaka, saboda haka mu kula da ita wannan dabba, wadda ta ke mu’amala a cikin gidajen mu, mu kula da abincin mu da abun shan mu, domin mu kauracewa wannnan illar da wannan dabba.

Idan mun gan ta a cikin gida, a yi kokarin kashe ta kuma a anbace sunan Allah (S.W.T) domin tana
tare da shaidanu don tana cutar da mutane.

*A yi amfani fa tsintsiya,

*ko takalmi wajen kashe ta

*ko kuma a sa mata maganin kashe kwari

Credit: Al'ummata

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN