Zargin saye wa budurwarsa waya: Mata ta kwara wa miji tafasashshen ruwan zafi (Hotuna)

Wata matar aure mai 'ya'ya hudu,ta shiga uku bayan ta kwara wa mijinta tafasashshen ruwan zafi bisa zargin cewa mijinta ya saye wa budurwarsa sabuwar wayar salula.

Bayanai sun ce matar Michael amajuoyi, wanda ke zaune a Nnaze a birnin owerri na jihar Imo, ta shaidawa abokin mijinta cewa " Bayan ya dawo daga wajen kasuwanci da dare, sai ya je ya shiga wanka, ni kuma na je na dauki wayarshi na fara buga gem, daga bisani sai wayar ta yi kara, sai na daga wayar, amma sai muryar wata yarinya ta ce na gode da wayar da ka saye mini, dama irin wayar da nike mafarkin samu ne. Na gode".


Matar Michael ta ce " Bayan yarinyar ta yi wadannan kalamai ne, sai kawai ta katse zance. Dama ina zargin mijina, sakamakon haka sai na je Kicin na tafasa ruwan zafi, na zo na same shi sai na kwara masa ruwan a bayanshi".

Abokin Michael ne ya garzaya zuwa Asibiti da shi, da misalin karfe  2 na dare, domin lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na dare.

Michael ya ce zai je Kotu domin ya nemi Kotu da raba aurensa da matarshi da zarar ya sami sauki.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN