Janar Babangida ya bayyana yadda za a kawo karshen boko haram


Rahotun Legit Hausa

Tsohon shugaban Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya yi hira da Jaridar Daily Trust a karshen makon nan, inda ya tabo batutuwa wanda su ka shafi harkar tsaro. A na sa shawarar, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewa ya kamata gwamnati ta dage wajen samun bayanan sirri game da yadda ‘yan Boko Haram su ke aiki.


Haka zalika tsohon Sojan Najeriyar ya nuna cewa akwai bukatar Sojojin Najeriya su san wanene manyan shugabannnin Boko Haram da kuma inda su ke samun horaswa. Ibrahim Babangida ya bayyana cewa Mayakan Boko Haram tsirarrun ‘Yan ta’adda ne kuma ba Sojojin yaki ba ne don haka su ke kokarin jefa tsoro a cikin zukatan ‘Yan kasa.

Bayan haka, tsohon shugaban kasar ya ce akwai bukatar a rika fadakar da jama’a tare da jan hankalinsu game ta’adin ‘Yan kungiyar, IBB ya ce wannan yaki na kowa ne. IBB wanda ya mulki Najeriya daga 1985 zuwa 1992 ya bayyana cewa dole sai kowa(Soja da farar hula) ya taka irin na sa rawar ganin wajen kawo karshen rigimar Boko Haram.

Janar Babangida ya bayyana cewa an dade ana samun rigingimu a Najeriya tun farkon kafuwar kasar. Sai dai tashin hankali ya yi kamari ne daga bayan zuwa Soji zuwa yanzu. A cewar Babangida, bayan yakin basasa a farkon shekarun 1970s, an yi ta fama da matsalar fashi da makami, amma da gwamnati ta tsaya tsayin-daka, sai da aka magance matsalar.

A hirar da ya yi da Daily Trust, tsohon shugaban kasar ya koka da yadda Dajin Sambisar da aka rika horas da Sojojin Najeriya a baya, ya koma hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram. A game da Dakarun Amotekun, Babangida ya nuna cewa akwai alamun cewa aiki ya yi wa Sojoji yawa. IBB kuma ya ce a lokacinsa, Hafsun Sojoji su na da wa'adin shekaru hudu ne, 


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN