Yanzu-yanzu: Kotu ta bayar da umarnin kama tsohon konturola janar na kwastam Dikko

Kotu ta bayar da umarnin kama tsohon Konturola janar na hukumar hana fasa kwabri na kasa Nigerian Customs Service (NCS), Abdullahi Indo Dikko, bayan ya kasa bayyana a gaban Kotun domin fuskantar tuhuma da ake yi masa, tare da wasu mutum biyu, da hukumar ICPC ta shigar bisa zargin damfara.
 
Jastis Ijeoma Ojukwu.ce ta vayar da wannan umarni ranar Litinin a babban Kotun tarayya da ke Abuja.

Jastis Ijeoma Ojukwu, ta ce Lauyan Dikko Solomon Akuma (SAN) , ya yi alkawarin cewa zai kawo Dikko gaban Kotu a zamanta na yau, amma sai ya gabatar da takardar cewa Dikko baya da lafiya., kuma an kwantar da  shi a wani Asibiti a birnin London.

Sakamakon haka, ta bayar da umarnin cewa jami'an tsaro su kamo Dikko su kawo shi gaban Kotu.
 
Ta ce, yayin da ake aiwatar da umarnin Kotu, idan an gano cewa gaskiya ne Dikko yana kwance a Asibiti a birnin London, Kotu za ta dakatar da umarnin kamoshi.
 
Ta kara da cewa, idan an sami akasin haka, masu kara su kamo Dikko, su kawo shi gaban Kotu ranar 16 ga watan Maris, 2020.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN