Wata matar aure mai suna Felicia Adikwu yar kabilar Jukun, ta shiga tsaka mai wuya tare da rudanin kunya, bayan ta bayyana cewa wanda mijinta ya dauko domin ya dinga koyar da yaransu karatu a gida ya yi mata ciki duk da aurenta.
ISYAKU.COM ya samo cewa Felicia tana cike da nadama kan wannan lamari, domin dai tuni aurenta ya fara fuskantar barazanan mutuwa.
Rahotanni sun ce Felicia ta yi karatu zuwa matakin Diploma a fannin shugabancin al'umma, daga bisani ta auri mijinta Joseph Adikwu wanda ya yi karatu a matakin HND, kuma yana aiki a wani Banki a jihar Nassarawa, kafin a sauya masa wajen aiki zuwa reshen Bankin da ke jihar Gombe.
Sun haifi yara biyu a aurensu na tsawon shekara tara. Suna da yara masu shekara 7 da biyar.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari