Dalibi na farko a makarantar horar da hafsoshin sojin Najeriya (NDA) ya rasu

Rahotun Legit Hausa

Dalibi na farko a makarantar horar da hafsoshin soji na Najeriya, Kanal Paul Ogbebor (Mai ritaya) ya rasu. Kanal Paul Ogbebor ya rasu ne yana da shekaru 80 a duniya bayan ya yi murabus daga gwagwarmayar aikin soja.

Ya kasance jarumi a yakin basasa na Najeriya. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar da takarda ta hannun mataimakinsa na musamman a fannin yada labarai, Femi Adesina, inda yake ta’aziyyar Ogbebor tare da tabbatar da cewa tarihin da ya kafa baya iya goguwa har karshen zamani. Kamar yadda takardar ta sanar; “Wannan ya bayyana zuwa karshen rayuwa da aka yi ta cike da hidimtawa kasa.

Tarihin da ya kafa ba zai gogu ba har karshen zamani,” shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar yayin ta’aziyyar Kanal Paul Ogbebor, wanda ya rasu yana da shekaru 80. Shugaban kasar ya tuna lokacin da Kanal Ogbebor ya zama dalibi na farko a makarantar horar da hafsoshin sojin Najeriya kuma yayi rayuwa mai cike da yi wa kasa hidima.

Yadda kuma ya nuna sadaukantakar shi a yayin da yayi yakin basasa. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa yankin da gogaggen sojan ya fito tare da shugabannin yankin. Marigayi Ogebebor ya saka sunansa cikin littafin tarihi na makarantar horar da hafsoshin sojin Najeriya.

Ya jajantawa iyalansa, danginsa, abokansa da kuma abokan aikinsa a kan wannan rashin. Yayi kira garesu da suyi alfahari da shi saboda rayuwa mai amfani da yayi wacce ta cika da nasarori masu yawa.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN