Mahaifiyar Leah Sharibu ta yi wa Landan tsinke don ganawa da Firaministan Birtaniya

Rahotun Legit Hausa

Mahaifiyar Leah Sharibu, yarinyar makarantar Dapchi daya tilo da ta yi saura a hannun yan ta’addan Boko Haram, Rebecca Sharibu ta isa Landan domin ganawa da Firaminista kan lamarin yarta. Misis Rebecca Sharibu wacce ta yi magana a wata hira da shafin BBC Hausa a Landan ta bayyana cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai damu da lbatun ceto yarta ba.

Sannan ta bayyana cewa, ta je Landan ne domin neman taimakon gwamnatin Birtaniya wajeen ceto Leah daga hannun yan ta’addan. A cewar Misis Sharibu, shugaba Buhari bai tuntubi iyalansu ba sai watanni bakwai bayan sace ‘yarsu.

Ta kuma yi korafin cewa, bayan Shugaban kasar ya tuntube ta, da kuma turo ministoci uku, inda ya bayar da tabbacin cewa za a saki Leah bad a jimawa ba, tun lokacin Shugaban kasar bai kara ce mata komai ba.

Ta kuma ce za ta kai kukanta ga Firaministan Birtaniya don tilastawa gwamnatin Najeriya kara himma wajen kubutar da 'yarta. Ta ce: “Tun da aka dauke su a watan Fabrairu amma sai watan bakwai na yi magana da Buhari ya ce Leah za ta dawo ba da dadewa ba kuma bayan sati biyu ya kara turo ministocinsa guda uku suka jaddada alkawalinsa.

"Sun karfafa min guiwa, amma daga waccan rana ban sake jin komi daga gwamnati ba. "Damuwa na kawai su yi kokari su fitar min da yarinyana. Mu 'yarmu muke so. "Ina jin ba dadi amma yaya zan yi tun da karfi na ba zai iya ba, kuma gwamnati ba ta yi komi ba.”

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN