Jami’an tsaro sun samo tarin makamai daga dajin wata jihar Arewa (Hotuna)

Rahotun Legit Hausa

Rahotanni sun kawo cewa jami’an tsaro da taimakon wani maharbi sun samo tarin makamai da alburusai wadanda ake zaton na yan fashi ne a dajin Lame-Burra, wani gagarumin maboyar miyagu a jahar Bauchi. A cewar maharbin, Ali Kwara wanda ya kasance tubabban dan ta’adda ne ya bayar da jawaban da ya kai su ga gano tarin makaman,

Channels TV ta ruwaito. Tarin makaman yan ta’addan, wanda aka baje a gidan gwamnatin auchi sun hada da alburusai sama da guda 1,000, makamai iri daban-daban guda 43 da kuma harsasai 30, koda dai su kansu yan ta’addan suna da yawa.

Gwamna Bala Mohammed wanda ya amshi makaman, inda shima ya mika wa yan sanda, ya ce gwamnatinsa ta yanke shawarar tattaunawa da al’umma a yaki da laifuffuka. Ya bayyana cewa an gano makaman ne sakamakon kwarewar hukumar tsaro ta SSS da sauran hukumomin tsaro.

“Tare da hadin gwiwar yan sanda, mun kwato wannan dagan yan bindiga da suka kasance da yawa sannan sun tsere daga Bauchi.“Akwai wasu yan leken asiri a ciki da wajen garin Bauchi da kewayenta wadanda suke taimaka mana wajen yin haka kuma wannan hadin gwiwa ne tsakanin gwamnati,

Ali Kwara da hukumomin tsaron saboda mu samu damar samun zantawa sosai da al’umma tare da wani kudirin sanin dukkanin wadannan yan bindigan,” in ji shi.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN