Zartar da hukuncin kotu: An kashe mayakan Boko Haram 10 ta hanyar bude musu wuta

Rahotun Legit Hausa

Dakarun sojojin kasar Chadi sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram guda goma ta hanyar bude mus wuta. An kashe mayakan ne kwana daya kacal bayan wata kotun kasar da ke birnin N'Djamena ta same su da laifin aikata ta'addanci kamar yadda ake tuhumarsu.

Majiyar jami'an tsaro ta bayyana cewa dakarun sojoji ne suka bude wa mayakan goma wuta a arewacin babban birnin jihar, N'Djemena. An gurfanar da dukkan mayakan goma ne a kan rawar da suka taka a wani hari da ya zama silar mutuwar mutane 38 a watan Yuni na shekarar 2019.

Bayan wata daya da kai harin ne kasar Chad ta gabatar da dokar kisa ga 'yan ta'adda. "Da safiyar yau (Alhamis) aka kashe su ta hanyar bude musu wuta," kamar yadda majiya ta sanar da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Daga cikin 'yan ta'addar da aka kashe akwai Mahamat Mustapha da aka fi sani da 'Bana Fanaye', wanda aka bayyana cewa shine ya kista harin da aka kai na watan Yuni. Mayakan Boko Haram sun kai harin ne a kan wani ofishin 'yan sanda da ginin makaranta da ke N'Djamena, lamarin da ya yi sanadiyyar raunata mutane fiye da 100 bayan wadanda suka mutu.

An kara samun fashewar bamabamai a wata kasuwa da ke babban birnin a watan Yuli, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 15. Hare haren ne na farko da mayakan kungiyar Boko Haram 'yan Najeriya suka kai kasar Chad, hedikwatar rundunar sojojin hadin gwuiwa.

Babban mai gabatar da kara, Bruno Mahouli Louapambe, ya shaida wa AFP cewa an samu mayakan 10 da laifukan da suka hada da hada baki, kisa, barnatar da dukiya ta hanyar amfani da sinadarai masu fashe wa, mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, amfani da miyagun kwayoyi da ke juya tunani da sauransu.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN