Rahotun BBC Hausa
Wata ma'aikaciyar jinya a Afirka ta Kudu na rawa saboda ta sanya marasa lafiya nishadi.
Jaridar
Daily Sun ta kasar, ta nuna hoton bidiyon ma'aikaciyar, Thathakahle
Gumede, 'yar shekara 57 tana ta taka rawa a gaban marasa lafiyan da suke
jira su ga likita a wani asibiti da ke KwaZulu-Natal.
Ms Gumede ta ce tana taka rawar ne domin marasa lafiyar da ke wajen su samu kwarin gwiwa a kan cutar da ke damunsu.
Ta
ce "Na yi amanna cewa magani ne ke warkar da ciwo, amma kuma mu ma
ma'aikatan jinya na da rawar ta kawa wajen warkewar marar lafiya".
Ms
Gumede ta ci gaba da cewa "Yana da matukar muhimmanci ma'aikatan jinya
su rinka yin abubuwan da za su sanyaya zukatan marasa lafiya, ba abin da
zai bata musu ba".
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Tags:
LABARI