An
daure wani matashi mai suna Kasim Khuram mai shekara 23 tsawon shekara
shida a Kurkuku, bayan ya karya kofar wajen da ake ma gawa ado kafin a
bizineta kuma ya yi lalata da gawar wata mata bayan ya karya marfin
akwatin gawa da aka saka ta a ciki, ya fito da gawarata ya yi lalata da
ita a dakin adon gawa na Co-Operative
undertakers a Titin Walsall, Great Barr da ke birnin Birmingham.
Yayin
da yake yanke masa hukunci a kan laifin da ya aikata, Alkalin Kotun
Birmingham Crown Court, Judge Melbourne Inman QC ya ce " Wannan ya saba
wa duk tunanin natsuwar kwakwalwan bil'adama, ban taba ji ko ganin irin
wannan danyen aiki ba, zai yi wuya a iya tunanin irin keta daraja da
mutuncin matacce da ka aikata".
Khuram ya shiga dakin
yi ma gawa ado ne da karfe 3 na dare, yayin da yake buge da ababen sa
maye na Manba da PCP kuma bayan ya kwankwadi Vodka. Ya yamutsa wasu
gawaki, ya kuma lalata jikin wasu gawakin mata guda biyu.
Khuram ya ya ce ya yi lalata da gawar wata mace, kuma ya amsa laifin karya kofofin dakin yi ma gawa kawa.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari