Idan kana mamakin yadda aka yi
budurwarka ta rabu da kai, watakila kana bukatar yin tunani da irin soyayyar da
ke tsakanin ka da ita. Yi la'akari da wasu dalilai wadanda 'yammata da yawa ba
sa so, wanda zai iya kawo karshen soyayyarku.
Soyayya ta gaskiya, ta na bukatar
yarda da juna, da kuma hakuri ta kowacce hanya. Amma idan ka aikata daya daga
cikin wadannan kurakuran, to akwai yiwuwar soyayyarku ta kusa zuwa karshe.
1. Rashin sannin yadda zaka
tarairayi budurwarka, ko ka dinga saka ta farin ciki.
2. Babu abinda ka iya sai tura mata
sakonni ta waya, eh an yadda cewa sako yana da amfani a wasu lokutan. Amma kuma
idan har tattaunawar da zaku yi ta na da yawa, abinda ya kamata kayi shine ka
kirata.
3. Ba ka bata hakuri idan kayi mata
laifi.
4. Rashin fada mata kalaman soyayya,
da yawan 'yammata suna son kalaman soyayya, suna so saurayi ya dinga koda su.
5. Yawan yi mata karya, maza da yawa
suna yi wa 'yammata karya, suna ganin kamar 'yammata sun fi kaunar mutum idan
ya yi musu karya. Hakan ba dai dai bane saboda duk ranar da ta gano ka, to
karshen soyayyarku ya zo kenan.
6. Rashin damuwa da sanin abokanta.
Ba dole sai ka so abokananta ba, amma ya na da kyau ka girma alakar da ke
tsakaninta da su, ya kamata su ma ka girmama su, saboda sune ginshikin
soyayyarku a wasu lokutan.
7. Ba ka yi mata tambayoyi idan ta
na magana da kai, yin shiru idan ta na magana ya na da kyau, saboda ya na nuna
mata cewa hankalinka ya na wurinta, amma kuma rashin yi mata tambayoyi shi ma
wata matsala ce a wurinta.
8. Rashin buri a rayuwa. Babu wata
mace da ke son namiji wanda ba shi da buri a rayuwarsa.
9. Yawan ba ta uzuri, irin su, baka
tashi da wuri ba, cunkuso ya rike ka da dai sauransu, mata ba sa son irin
wannan uzurin.
10. Yawan yi mata maganar tsohuwar
budurwarka. Duk namijin da ya fiya yiwa mace maganar tsohuwar budurwarsa, to ya
tabbata cewa soyayyarsu ta kusa karewa da budurwarsa.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari