Barawo ya sace jakar kudi da 'yansanda ke aje kudin cin hanci, duba abin da ya faru

Rahotun Legit Hausa

File picture
An yi wani karamin lamari da yayi kama da almara a ranar Laraba, 19 ga watan Fabrairu tsakanin ‘yan sanda da kuma wani barawo. Barawon ya wabce jakar da ‘yan sandan suka zuba cin hancin da suka samu a kan titi sannan ya shige daji da gudu.

Kamar yadda jaridar Tuko.co.ke ta ruwaito, lamarin ya faru ne kusa da wani babban shago na Kathegeri da ke babbar hanyar Nairobi zuwa Meru. Jaridar The Pulse.ng ta bayyana cewa barawaon ya fito ne daga cikin daji, inda ya kwace kudin da ‘yan sandan suka tara sannan ya shige dajin da ke kusa dasu a guje.

Jaridar Nairobi News ta ruwaito cewa wani ganau ba jiyau bane ya sanar da cewa ‘yan sanda biyu ne mace da namiji ke kan titin a yayin da aka musu fashin. “Akwai wata hanya ce da ta hada titin da dajin. Ta nan kuwa ‘yan sandan ke tsaye amma ta bangaren titin.

Daga ciki barawon ya bayyana tare da wabce jakar kudin cin hanci da suka tara. Ganin ba zasu iya kamo shi bane yasa suka dinga zagin shi,” ganau din ya sanar. Wanda lamarin ya faru a gaban shi ya ce dan sandan ya yi yunkurin damko barawon amma hakan bai samu ba saboda yanayin wajen. Hakazalika ‘yan sandan rike suke da kulki ba bindiga ba.

Hakan ne kuwa yasa suka dinga dura mishi zagi. Kafin su rasa kudaden da suka tara, jami’an ‘yan sandan sun dinga tsayar da motoci inda suka dinga karbar kudi daga wajen mutane. Cikin kuwa sa’o’i kasa da biyar barawon ya kwace ‘gumin’ ‘yan sandan.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN