Kunkuru mai shekara 100 mai ’ya’ya 800 zai koma gidansa na asali

Rahotun Jaridar Aminiya

Wani tsohon kunkuru mai shekara 100 mai suna Diego da ke rayuwa a Tsibirin Galapagos da ke Kudancin Amurka, wanda aka yi amfani da jinsinsa wajen haifar sama da kunkuru 800, yanzu haka za a mai da shi gidansa na asali.

Jaridar Daily Mail ta Ingila ta ce, tun asali an kai Diego Tsibirin Galapagos ne don amfani da maniyyinsa wajen samar da jinsi irin nasa kuma za a mai da shi ne tare da wasu masu jinsi irin nasa da aka haifa su 14, kamar yadda Hukumar Kula da Gandun Daji ta  Galapagos National Parks (PNG) ta sanar.

Kunkuru Diego, ya bada gudunmawa sosai wajen shirin Tsibirin Santa Cruz Island da aka yi a Jihar Kalifoniya, don haka ma’aikatan da ke kula namun dajin suka maida hankali a kan jinsin Diego, inda suka sanar da cewa jinsinsa ne ke da kashi 40 cikin 100 na duk halittar kunkuru dubu 2 da za a iya samu.

Daraktan Gidan Adana Namun Dajin, Jorge Carrion, ya ce: “Kimanin kunkuru 1,800 suka dawo garin Espanola, kuma yanzu haka an samu jinsi halittar Diego 2000.

“Hakan na nuna cewa su ma suna iya haifar irin jinsin Diego, kuma za su iya rayuwa a yanayin halittar Diego,” inji shi.

Kimanin shekara 50 da suka gabata jinsin maza biyu irin Diego kawai ake da su da kuma mata 12 da suke rayuwa a garin Espanola, amma yanzu haka suna ci gaba da yaduwa a sassan duniya.
An kawo Diego ne daga gidan adana dabbobi (Zoo) na San Diego da ke Jihar Kalifoniya, don shiga cikin shirin barbarar dabbobi da aka yi a tsakiyar shekarun 1960 don habaka jinsinsa.

Amma yanzu ana shirin mai da shi gidansa na asali, inda ya rayu shekaru masu yawa a gidan Zoo na San Diego.

Mista Jorge ya ce: “Diego ya taimaka wajen yaduwar irin jinsinsa don haka ake shirin maida shi Espanola.

A yanzu haka jama’a da dama na murnar mai da kunkurun garinsa na asali.”

Nauyin Diego ya kai kilo 80, sannan tsawonsa a kwance ya kai santi mita 90 sai tudunsa ya kai mita 1.5 idan ya bude kafafunsa da wuyansa.

Kafin a kai kunkurun zuwa Espanola, an takaita zirga-zirgarsa na wani lokaci don kauce wa cinye irin wasu tsirrai da aka shuka a tsibirin.

Tsibirin Galapagos na Ecuador, yana yankin tekun Pacific ne, hakan ya sa Charles Darwin mai nazarin jinsin halittu ya yi bincike na musamman a kan irin wadannan halittu.

A irin wannan rahoto ne  kan Diego, wani mai nazari na musamman mai suna Lonesome George, ya fitar da wani rahoton wani tsohon kunkuru da yake rayuwa a Galapagos shekaru da dama, amma ya ki yin barbara tun lokacin da aka kebe shi a waje guda.

Bayan fitar da irin wannan rahoton kunkurun Lonesome George, ya rasu a shekarar 2012 wanda shi ma ya wuce shekara 100.

Akwai tsibirai da suka kai 21, amma guda hudu ne kadai halittu za su iya rayuwa da adadinsu ya kai dubu 25.

A wannan tsibiri akwai sama da halittu 1,300 wadanda ba a iya samunsu a ko’ina a duniya sai a tsibirin, yanzu haka yana tsakiyar tekun kusa da birnin Makka.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN