Yadda wata mata ta mutu bayan kammala zina da saurayinta dan sanda

 Rahotun Legit Hausa

Wata mata wacce har yanzu ba a san kowacece ba ta rasa ranta bayan jerin kwanciyar da suka gama da masoyinta kuma dan sanda a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti. Lamarin ya faru ne a dakin wacce ta rasun da ke titin Atayese a rukunin gidaje na Baawa da ke Ado Ekiti a daren Laraba.

Tuni dai ‘yan sandan suka damke saurayin na ta wanda aka gano ya zo daga Legas ne inda yake aiki a matsayin dan sanda, kamar yadda jaridar the Nation Online ta ruwaito. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce wani makwabcin mamaciyar ne ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda da ke Oke a babban birnin jihar.

Hakan kuwa yasa jami’an tsaro suka dau matakin gaggawa. Ya ce, “Budurwar ta mutu ne a cikin dakinta kuma wani makwabcinta ne ya sanar da ‘yan sandan Oke Ila da ke Ado Ekiti. Jami’an tsaro sun gaggauta zuwa gidan kuma sun samu gawar matar.

Tuni dai aka dauke gawar kuma an ajiyeta a ma’adanar gawawwaki da ke assibitin koyarwa na Ekiti.” Abutu ya kara da cewa an kama wanda ake zargin da kasheta kuma a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda. Amma kuma ya ce gane mutumin da aikinsa ne har yanzu ba a yi ba don ana ci gaba da bincike.

 “Har yanzu dai ba mu tabbatar da cewa dan sanda ne ko a’a. Muna jiran sakamakon bincikenmu wanda zai bayyana hakan”, Abutu ya ce. A wani rahoto na daban, Wani mutum da ake zargi da amfani da maganin karin kuzari ya mutu a wani otal da ke Onitsha a jihar Anambra.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, mutumin ya isa dakin otal din a Onitsha tare da wata budurwa, amma sai budurwar ta fito tana ihun neman taimako. A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra, SP haruna Mohammed ya ce wajen karfe 12:03 na safiyar 24 ga watan Fabrairun 2020, manajan Plus View otal da ke Onitsha ya kawo koken mutuwar wani a dakin otal dinsu. Paul Okwudili mai shekaru 40 a duniya na Ogboliolosi da ke babban titin Awka a Onitsha ya kai wata budurwa dakin otal kuma ya mutu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN