Tambayoyi da amsoshi 100 domin mata (1)

Rahotun Jaridar Aminiya
Tambayoyi a kan tsarki da jinin Haila da na Biki
Tambaya ta 1: Shin mace mai jinin biki za ta zauna har kwana arba’in (40) ne ba za ta yi Sallah ba kuma ba za ta yi Azumi ba, ko kuma abin Iura daga gare ta za ta yi tsarki, ta yi Sallah kuma nawa ne mafi karancin kwanakin da za ta yi kafin ta yi tsarki?

Amsa: Mace mai jinin biki ba ta da kayyadajjen lokaci sai dai duk Iokacin da jinin ya zo mata za ta zauna ba za ta yi Sallah ba kuma ba za ta yi Azumi ba kuma mijinta ba zai iya saduwa da ita ba. Amma idan ta ga jinin ya dauke, wato ta tsarkaka ko da kafin ta cika kwana arba’in ne ko da jinin iyakacin kwana goma kawai ya yi ko kwana biyar kawai sai ya dauke, to sai ta yi wanka (na tsarki) ta yi Sallah, ta yi Azumi kuma mijin ya zo mata babu laifi a cikin haka.

Sai dai abin da ya fi muhimmanci shi ne shi jinin biki al’amari ne kebantacce kuma hukuncinsa yana ratayuwa ne da shi, wato idan jinin ya zo to hukuncinsa yana nan ba za ta yi Azumi da Sallah ba. Kuma idan jinin bai zo ba to hukuncinsa baya nan.

Duk lokacin da ta yi tsarki to ta wofanta daga hukuncinsa. Sai dai idan jinin ya karu matar ta zamo mai jinin Istihala, wato jinin ciwo ke nan, sai ta yi lissafin iya kwanakin bikinta, ta yi wanka ta yi Sallah. Sai ta nemi maganin wannan jini na cuta.

Tambaya ta 2: Mai tambaya yana cewa: Mace ce bayan an yi mata aure da wata biyu bayan ta yi al’ada ta yi tsarki sai kuma ta fara ganin wani digon jini kadan; to shin wannan matar za ta sha Azumi ne idan lokacin Azumi ne ko kuma me za ta aikata?

Amsa: Mas’aIoIin mata a cikin aI’ada da aure kogi ne wanda ba ya da iyaka sai dai ka’ida ta gaba daya cikakkiya ita ce idan mace ta tsarkaka ta ga tsarki tabbatacce daga al’adarta – wato fitar wani farin ruwa bayan daukewar jinin al’ada, to idan wani bakin jini ya zo bayan ta ga wannan farin ruwan ko wani fatsi-fatsi ko wani dan digon jini ko wani danshi, to duk wadannan abubuwa ba haila ba ne kuma ba ya hana Azumi da Sallah da jima’i domin shi ba haila ba ne.

Ummu Adiyya (RA) ta ce “Mu ba ma kirga baki da kankanen jini wani abu (wato ba mu dauka haila ba).” Bukhari ne ya fito da Hadisin. Abu Dauda kuma ya kara da cewa idan bayan mace ta yi tsarki tabbataccen tsarki sai ta ga daya daga cikin wadannan abubuwa to ba zai cutar da ita ba kuma ba zai hana ta Sallah da Azumi da saduwa da mijinita ba.

Sai dai yana wajaba a kan mace kada ta yi gaggawa wajen yin wanka har sai ta ga tabbataccen tsarki domin wadansu matan daga sun ga jini ya bushe a gabansu sai su yi gaggawar yin wanka tun kafin su ga farin ruwan ko daukewar jinin gaba daya.

Don haka ne matan sahabbai suke aikawa wajen Uwar Muminai A’isha, (Allah Ya yarda da ita), suke aikawa da auduga ajikin audugar kuma suna shafa jini sai ita kuma ta ce musu kada ku yi gaggawa har sai kun ga farin ruwa sannan ku yi tsarki.
 
Tambaya ta 3: Mai tambaya yana cewa: Mene ne hukuncin samuwar mace a cikin Masallaci Mai alfarma alhalin tana haila don sauraron Hadisai da hudubobi?

Amsa: Ba ya halatta ga mace mai haila ta zauna a cikin Masallaci Mai alfarma ko wanin wannan masallaci daga cikin masallatai, sai dai yana halatta a gare ta ta wuce ta masallacin ko kuma ta dauki wani abu a cikin masallacin da makamantan haka, kamar yadda Annabi (SAW) ya ce wa A’isha (RA) yayin da ya umarce ta da ta dauko masa darduma, sai ta ce masa ai dardumar tana cikin masallaci ita kuma ga shi tana haila, sai Annabi (SAW) ya ce mata ai hailar ba a hannunki take ba (wato za ta iya shiga masallacin don ta dauko dardumar).

Idan mace mai haila ta wuce ta cikin masallaci ta tabbatar cewa jinin ba zai zuba ba a ciki ba, to babu laifi a kan haka. Amma idan tana nufin ta shiga ta zauna a masallacin ne to bai halatta ba.Dalilin haka kuwa shi ne Annabi (SAW) ya umarci mata su fita zuwa wurin Sallah lokacin Sallar ldi ya umarci ’yan mata da tsofaffi da ’yan mata da masu haila sai dai masu haila ya ce su fita daga cikin filin Sallah su je gefe. To wannan yana nuni a kan ba ya halatta ga mace mai haila ta zauna a masallaci don sauraron huduba ko don sauraron darasi ko hadisai.

Tambaya ta 4: Shin yana wajaba ga mace mai jinin biki ta yi Azumi, ta yi Sallah idan jini ya dauke mata kafin kwana arba’in?

Amsa: Eh, idan mace ta samu tsarki, jinin biki ya dauke mata kafin kwana arba’in yana wajaba a gare ta, ta yi Azumi idan ya kasance a cikin Ramadan ne, kuma ya wajaba a gare ta ta yi Sallah. Kuma ya halatta ga mijinita ya sadu da ita, domin ta tsarkaka, ba ta tare da abin da zai hana ta yin Azumi da Sallah kuma ya halatta a sadu da ita.

Za a iya samun Ahmad Adam Kutubi (SP) ta 08036095723

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN