Fiye da mutum 20,000 a Zamfara sun canja sheka daga APC zuwa PDP

Jam'iyar APC a jihar Zamfara ta yi asarar kimanin mambobinta guda 20,000 bayan sun canja sheka zuwa jam'iyar PDP.
 
Jaridar DailyPost ta ruwaito cewa wadanda suka canja shekan sun fito ne daga kananan hukumomin Bakura da Gummi.
 
Yayin da yake karbar wadaanda suka canja shekan a gidan Gwamnati da ke Gusau, Gwamna Bello 
 Mohammed Matawalle ya ce wannan babban asara ne ga jam'iyar APC a jihar.
 
Matawalle ya yi kira ga al'umman jihar Zamfara, su bayar da nasu gudunmuwa domin ci gaban jihar, ba tare da la'akari da banbancin siyasa ba.
 
Ya ce Gwamnatinsa ta dukufa wajen ganin ta samo kwararru da masana domin ganin cewa an ciyar da jihar gaba.

DAGA ISYAKU.COMLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN