Buhari ya amince da fadada babban titin Abuja zuwa Kano don daukan motoci 6 a jere

Rahotun Legit Hausa
Majalisar zartawar gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da kara fadada babban titin Abuja zuwa Kano da ya ratsa ta jahar Kaduna daga hannuwa 4 zuwa hannuwa 6.
Daily Trust ta ruwaito ministan ayyuka, Babatunde Raji Fashola ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru bayan kammala taron majalisar zartarwa a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa.
Ministan yace majalisar ta amince da baiwa kamfanin Yolas Consultant kwangilar gudanar da wannan aiki a kan kudi naira miliyan 867.263, wanda ake sa ran kammala shi cikin watanni 5 masu zuwa, sa’annan yace aikin zai kunshi gina manyan gadoji guda 66.
A hannu guda kuma, majalisar ta amince da wasu bukatu biyu da ma’aikatar sufuri ta mika mata na gudanar da gyare gyare a tashar jirgin ruwa na Tincan Island, tare da kwangilar daukan wasu ma’aikatan ruwa guda 180.
Karamar ministar sufuri, Gbemisola Saraki ta bayyana cewa gwamnati ta bayar da kwangilar ma’aikata 180 ga kamfanin Messr AG Vision Nigeria Limited a kan kudi naira biliyan 1.482, yayin da kwangilar gyaran Tincan aka baiwa Messrs Yolas Consultant a kan kudi naira miliyan 144.
A wani labarin kuma, hukumar majalisar dokokin Najeriya ta bayyana damuwarta game da yiwuwar kungiyar ta’adda ta kaddamar da harin ta’addanci a majalisa, kamar yadda wani babban jami’in hukumar ya bayyana.
Wannan jami’I da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa: “Da gaske ne, mun samu mummunan rahoton tsaro dake bayyana cewa majalisar dokokin Najeriya na daga cikin wuraren da yan ta’adda ke shirin kaddamar da hari, kuma ba na wasa bane.”
Jami’in yace suna yawan samun bakin fuskoki dake shiga cikin majalisa a yan kwanakin nan, kuma hakan ya zama abin damuwa ga hukumar majalisar, kamar yadda ya shaida ma majiyar Legit.ng.
Jami’in ya kara da cewa a lokutta da dama da zarar jami’an hukumar ko jami’an tsaro sun tunkari wadannan bakin fuskoki game da dalilin zuwansu majalisar sai su ce sun zo wurin wakilansu ne, bugu da kari jami’an tsaron majalisar sun yi karanci.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN