Kai tsaye: Kotu ta kama tsohon kakakin PDP da laifin almundahanan N400m, ana kan yanke masa hukunci

Rahotun Legit Hausa

Babbar kotun tarayya dake Abuja, a ranar Talata, ta kama tsohon kakakin jamiyyar Peoples Democratic Party PDP, Olisah Metuh, da kamfaninsa, Destra Investments Limited, da laifi daya cikin bakwai da hukumar EFCC take zarginsa da su.

Yanke hukunci kan zargi na farko, Alkali Okong Abang ya yanke ceewa tsohon mai baiwa shugaban kasa shawarar tsaro, Sabo Dasuki, ya baiwa Olisah Metuh kudi N400m a Nuwamba, 2014.

Alkalin ya bayyana cewa ya kamata Olisa Metuh da kamfaninsa su sani cewa kudin haram aka basu saboda ba su da wata alaka da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawarar tsaro.

Alkali Okong Abang ya yi watsi da jawabin lauyoyin Metuh na kan cewa ba zaa iya kamashi da laifi ba tunda har yanzu ana shariar Sambo Dasuki da ya bashi kudin. A

 yanzu haka, Alkalin na cigaba da karanto shariarsa kan sauran laifuka shida da ake zargin Olisa Metuh da su.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN