Majiyar isyaku.com ta ce Jackson ne ya dauki nauyin karatun budurwarsa Christine tun da ta gama makarantar sakandare har zuwa makaranta na gaba da sakandare. Makonni uku da suka gabata, Jackson tare da budurwarsa Christine, sun fice daga gidan da suke haya saboda Jackson ya kasa biyan kudin haya.
Sakamakon haka sai ya laba a wajen abokansa, ita kuma Christine ta laba a wajen kawarta, inda a nan ne ta fara cin amanar saurayinta Jackson Mwanza bayan ta fara soyayya da wani bakanike, wanda ganin haka ke da wuya Jackson ya bindige bakaniken da bindiga har lahira, ya harbi kawar budurwarsa da bindiga a kafada, ya kashe mutum biyu, kuma ya raunata wasu mutum biyu kafin ya juya bindigar ya bindige kanshi har lahira.
Wata majiya ta kara da cewa, budurwar Jackson har ila yau, bayan soyayya da take yi da wannan bakanike, hakazalika tana soyayya tare da wani saurayi a makaranta da Jackson ya ke biya mata kudi a Chianama.
Yanzu haka yansanda sun damke Cristine suna yi mata tambayoyi dangane da hakikanin abin da ya faru da ya sa Constable Jackson Mwanza ya kashe kanshi.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari