Jami'an rundunar yan sandan jihar Katsina sun yi nassarar halaka wasu masu satar mutane, tare da fashi da makami da suke addaban bayin Allah a yankin Malumfashi, Faskari, Dandume, Bakori, Kankara da karamar hukumar Sabuwa a jihar Kano da Zamfar.
Kwamishinan yansandan jihar Katsina CP Sanusi Buba, ya shaiada wa manema labarai haka a Karsina ranar Litinin.
Ya ce an bi sawun masu aaikata laifin ne, lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wajen da zasu aikata laifi a karamar hukumar Gwarzo ajihar Kano.
Ya kara da cewa wadanda aka kama su ne: "Hassan Fulani Audu mai shekara 30 daga kauyen Kadawa a karamar hukumar Dandume na jihar Katsina, Ahmadu Lawal dan shekara 19 daga kauyen Maska a karamarhukumar Funtua jihar Katsina, da Iliyasu Alh Adamu alia Yello mai shekara 28 daga Bakin
Dutse, Jibiri, a karamar hukumar Funtua na jihar Katsina , Nura Abdullahi mai shekara 22 daga kauyen Yar-Tafki, a karamar hukumar Funtua na Katsina, da kuma Ahmed Abdullahi, dan shekara 25 daga kauyen Yar-Tafki a karamar hukumar Funtua na jihar Katsina.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari