Fim din Indiya na farko da aka yi da bakar fata mai suna 'Namaste Wahala' ya fita

 Rahotun Legit Hausa

Hamisha Daryani Ahuja 'yar kasuwa ce a kasar India wacce ta koma sana'ar fim. Ta saki fim dinta na farko mai suna 'Namaste Wahala'. 'Namaste Wahala' fim ne wanda babu dadewa zai fito kuma ya samu umarnin Hamisha Daryani Ahuja ne, kamar yadda jaridar Pulse ta ruwaito.

'Yar kasar India amma mazauniyar jihar Legas din za ta fitar da fim din ne mai dauke da 'yan masana'antar Nollywood mai suna Ini Dima-Okoji. Hamisa ta bayyana a shafinta na Instagram a watan Janairu cewa za ta fada harkar fim tare da nuna yadda zai kasance.

Ta ce zai taba al'adun kasar Indiya ne da na Najeriya. Ta wallafa "babu komai sai sha'awar hada fim na shiga masana'antar. Zan fitar da fim wanda zai bayyana al'adun kasar Indiya da na Najeriya.

A lokacin da na fara wannan tunanin, na san akwai bukatar aiki tukuru tare da mayar da hankali sannan in ga hakan ta faru." Kamar yadda jarumar fim din, Ini Dima-Okojie ta ce an kammala daukar fim din 'Namaste Wahala'.

Hakan na nufin yana gab da fitowa kenan. Sabon fim din ya kunshi taurari kamar Ajoke Silva da Richard Mofe Damijo. Akwai Broda Shaggi da mawaki MI Abaga.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN