Rahotun Legit Hausa
Mawakin yabo na addinin Kirista a kasar Rwanda, Kirito Mihigo, wanda aka taba kamawa da laifin kokarin kashe Shugaban kasa Paul Kagame ya rasu. Kamar yadda 'yan sanda suka sanar, Mihigo mai shekaru 38 ya kashe kan shi ne a yayin da yake tsare wajen 'yan sanda.
An yanke mishi hukuncin shekaru 10 a gidan yari ne bayan da aka kama shi da laifin hada kungiyar 'yan daba, hada kai wajen kisan kai da kuma hada kai don cutar da gwamnati tare da Shugaban kasa. An yafewa Mihigo a 2018 amma sai aka kara kama shi a makon da ya gabata yayin da yake kokarin tsallakawa zuwa Burundi.
Hukumomi sun sanar da cewa wannan karantsaye ne ga sharuddan rangwame, kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito.
"Jami'an tsaro sun adana shi na kwanaki uku yayin da suke binciken dalilin tsallake iyakar ba tare da bin ka'ida ba da kuma zargin cin hanci", mai magana da yawun 'yan sandan Eric Kabera ya sanar a takardar. Ya kara da cewa, an bar Mihigo ganawa da iyalansa tare da lauyansa ko a lokacin da yake tsare.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari