Dubban mata da matasa sun mamaye titunan Yenagoa bayan Koto ta kori Gwamnan APC

Zanga zanga ta barke a Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa, bayan Kotun koli ta kwace kujerar Gwamnan APC Chief David Lyon ta ba wa PDP.
Jaridar Vanguard ta labarta cewa, dubban mata sun bazama a titunan birnin Yenagoa, suka dakile wasu hanyoyi, suna cewa "Ba Lyon ba Bayelsa, kuma ba za a mika mulki idan ba ga Lyon ba a jihar Bayelsa"

Wasu matasa suna rike da tutocin jam'iyar APCsuna kadawa suna wake waken nuna goyon baya ga APC da Lyon, suka mamaye tituna sakamakon haka suka haifar da cinkoso domin sun tare masu amfani da ababen hawa sakamokon bajewa da suka yi a tituna. .
A wani labarin daban, mun samo cewa wasu matasa da ake zargin cewa magoya bayan jam'iyar APC ne, sun je gidan sabon Gwamna kuma suka farfasa motoci tare da barnata wani sashe na gidansa a birnin Yenagoa.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN