Buhari ya shiga ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaro, babu Monguno (Hotuna)

Rahotun Legit Hausa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, ya shiga taro na musamman tare da sifeta janar na 'yan sanda da shugabannin tsaron kasar nan. An yi taron ne a fadar shugaban kasa a Abuja, babban birnin tarayya.


Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban tsaro Janar Gabriel Olonisakin, shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, shugaban sojin sama, Air Marshall Sadique Abubakar, shugaban sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas. Sifeta Janar din 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya samu damar halartar taron, wanda aka yi yayin da ake tsaka da fuskantar kalubalen tsaro a kasar nan.

Amma kuma mai bayar da shawara a kan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, baya nan. Buhari da shugabannin tsaron suna yin taruka a kan tsaro kusan kowanne mako, amma dai na yau an kirasa da na musamman.Shugabannin tsaron sun wuce ta ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar, Abba Kyari, a yayin da suke ficewa bayan kammala taron Buratai ne na karshe da aka gani ya bar wajen da misalin karfe 3:55 na yamma.

A cikin kwanakin nan ne aka matsantawa Buhari a kan ya sallami shugabannin tsaron kasar nan sakamakon kalubalen tsaron da kasar nan ke ci gaba da fuskanta Hatta majalisar dattijan kasar nan sun yi kira ga shugaban kasar a kan ya sallami shugabannin tsaron.

Amma kuma, har yanzu shugaban kasar yayi biris da wannan kiran, tare da cewa mulkinsa ba zai dau mummunan mataki a kan shugabannin tsaron da suka dinga kokari tun 2015 ba.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN