Sau da yawa akan ji labarain cewa mutum ya yanke jiki ya fadi ya mutu, yayin da yake wajen aiki, ko wani waje da ya je domin gudanar da wata lalura ko lamari na yau da kullum, kwatsam sai a ji labarin cewa ya fadi ya mutu.
Bincike ya nuna cewa, akasarin irin wannan mutuwa, hawan jini ne ke haddasawa, musamman idan mutum yana fama da cutar hawan jini amma bai sani ba, jinin zai yi ta hauhawa har ya wuce ka'ida.
Likitoci sun ce kada yawan gudun jini a jikin dan Adam shi ne 90/139 a bisa daidaita, fiye da haka kuwa a maimaicin lokutta yana nufin mutum ya kamu da hawan jini.
Cutar hawan jini ana iya gadonta daga iyaye da kakanni a cikin zuri'a, haka zalika salon rayuwan dan Adam zai iya haifar da hawan jini ga mutum, misali, shan taba sigari, barasa, rashin motsa jiki, yawan cin kitse ko maiko, yawan shan gishiri a abinci musamman wanda ba a dafa ba da sauransu.
Ga mutane da ke da tarihin shanyewar bangaren jiki a daya daga cikin yan zuri'arsu, ko an taba samun wanda ya yanke jiki ya fadi ya mutu, ko haka kawai yana cikin Sallah, tafiya, zaune ko kawai ana hira da shi amma lokacin da ya yunkura ya tashi sai ya yanke jiki ya fadi ya mutu da sauran ire-iren wandannan matsaloli. Ya zama wajibi masu irin wannan tarihi a zuri'a su dinga auna jininsu a Asibiti akalla sau daya a kowane wata shida, har ma dai idan an kai shekara 40/45 ko fiye, musamman ga maza.
Dr. Aminu Muhammad ya ce , kididdiga ya nuna cewa maza sun fi mata yawan kamuwa da cutar hawan jini a Duniya, haka zalika ya ce jinsin bakaken fata sun fi turawa yawan masu fama da cutar hawan jini a Duniya. Haka zalika ko a Najeriya.
Rahotun Isyaku Garba Zuru
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari