Da sanyin safiyar Laraba, wata babban mota ta buge wani dansanda, kuma ta bi ta kansa ta takeshi, yayin da yake aikin tsayar da motoci domin bincike a babban titin Owerri zuwa Okigwe a jihar Imo.
Wannan lamari ya faru a garin Atta a cikin karamar hukumar Ikeduru, sakamakon haka, jama'a suka shiga fargaba da tsoron abinda zai je ya dawo.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an ga gawar dansandan a gefen titi, yayin da sauran jami'an tsaro fusace rike da bindigogi suka hana jama'a isa kusa da gawar.
Hakazalika an ga wasu manyan motoci bayan yansanda sun tsayar da su a wajen da lamarin ya faru.
Bayanai sun ce motar tana tafe a guje, sai dansandan ya tsayar da ita, amma sai ta bi ta kanshi bayan ta buge shi.
Kakakin hukumar yansandan jihar Imo Orlando Ikeokwu ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce hukumar na daukan mataki da suka dace kan lamarin.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari