Yadda EFCC ta yi diran mikiya a ofishin jindadin Alhazai na jihar Kebbi

Rahotun Legit Hausa
Mun samu labari cewa hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa sun aukawa hukumar kula da jin dadi da walwalan Alhazai na jihar Kebbi.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa EFCC ta na zargin hukumar Alhazan jihar da kin dawowa da wasu rarar kudin da aka samu daga aikin hajjin daka ayi a shekarar 2017/2018.
Kudin da ake zargin hukumar Alhazan da lamushewa zai kai Naira miliyan 90. A samamen da EFCC ta kai a ofishin, ta iya gano wasu daga cikin wannan kudi inji wani Jami’i.
Shugaban hukumar EFCC na Yankin Sokoto, Kebbi da Zamfara, Mista Abdullahi Lawal, ya shaidawa ‘Yan jarida wannan a jiya Ranar Litinin, 10 ga Watan Fubrairun 2020.
Abdullahi Lawal ya kuma tabbatarwa Manema labarai cewa EFCC ta gayyaci shugaban kwamitin maida kudin aikin hajji da Darektan harkar kudi domin yi masu tambayoyi.
Haka zalika Hukumar ta EFCC ta kira Mai kula da asusun kudin hukumar Alhazan ya yi bayani game da yadda aka batar da ragowar kudin Maniyattan Kebbi na shekarar.
“Hukumar Alhazai na kasa ta dawowa Mahajjata da kudinsu ta hannun hukumomin jihohi, kuma aka sanar da mu. Akwai bukatar ace an maidawa kowa ragowar kudinsa.”
“Ya kamata ace hukumar ta maidawa wadanda su ka sauke farali a shekarar 2017/2018 a Saudi Arabia kudinsu, amma babushaidar da ke nuna cewa an maida kudin.”
“Wannan ya sa mu ka shigo da karfinmu domin ganin inda aka samu matsala, ko meyasa har yanzu Mahajjatan jihar ba su samu kudinsu bar har yau.” Inji Mista Lawal.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN