Rahotun Legit Hausa
Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da sakataren din-din-din na
ma’aikatar ayyukan a jahar Nasarawa, Alhaji Jibrin Giza, a tsakar daren ranar
Asabar. Kwamishinan yan sanda a jahar, Mista Bola Longe, ya tabbatar da lamarin
ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a Lafia.
Longe ya fada ma NAN cewa yan bindiga sun sace sakataren
din-din-din din daga gidansa a Shabu, wani yanki na Lafia da misalin 12:40 na
tsakar dare zuwa wani wuri da ba a sani ba. A cewar kwamishinan yan sandan,
Shugaban yan sanda a yankin ya rigada ya zuba wasu jami’ai wadanda za su bi
sahun masu garkuwan da suka tsere da wadanda suka sace.
Longe ya kara da cewa ya umurci mataimakin kwamishina na
ayyuka, jami’in da ke kula da rundunar yaki da fashi na musamman, da su kakkabe
yankin don tabbatar da sun ceto wadanda aka sace da kuma kama masu garkuwan. Ya
kuma sha alwashin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta ceto
wadanda aka sace. Longe ya kara da cewa masu garkuwan ba su kira yan’uwan
wadanda suka sace ba tukuna.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari