Mazauna
wani kauye a kasar Zambia sun wayi gari cikin ganin wani abin al'ajabi a
yayin da wata Mata mai shekara 40 ta bukaci Kotun garin ta daura mata
aure da dan da ta haifa mai shekaru 23.Matar dai Madam Mbereko ta bukaci
a daura masu aure ne da dan nata Farai Mbereko a cewar ta domin sun
tsunduma cikin soyayya shekaru uku da suka wuce.
Rahotanni
sun nuna cewa Alkalin Kotun garin bai aminta da wannan auren ba,a
sanadin haka ma'auratan suka je wani gari aka daura masu aure.A nata
bayanin,Uwar sabon mijin nata kuma dan ta Farai,cewa ta yi bayan rasuwar
uban shi dan nata Farai,ta sha matukar wahala wajen biya masa kudin
makaranta har izuwa wannan lokaci da Allah ya sa ya zama abin da ya zama
a yanzu,"babu wanda ya taimaka min wajen shan wahala da shi kuma ba zan
bari haka kawai wata mace ta more shi ba daga sama" in ji Mbereko uwar
mijin ta.
Wani dattijo mazauni wannan kauyen cewa yayi
"idan a lokacin da ne,ita Uwar da Dan nata za'a kashe su ne a bisa
al'ada domin hakan yakan janyo bala'i a kauyen.Amma da yake muna cikin
wani zamani na tsoron 'yan sanda ya zama wajibi mu yi korafi
kawai".Wannan Matar dai a yanzu haka tana dauke da cikin sabon Mijin
nata kuma Dan ta na cikin ta.To jama'a...wannan Da ne kenan ake shirin
haifawa ko Jika ?
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari