Za mu dauki fansar ran Janar Qasem Soleimani da Amurka ta kashe - Iran

Rahotun BBC Hausa

Jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana cewa "za a dauki mummunar fansa" kan wadanda suka kai harin da ya hallaka babban kwamandan Iran.

Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta hallaka kwamandan zaratan sojojin juyin-juya hali na Iran, Qasem Soleimani, a wani harin sama da sojojinta suka kai kan filin jirgin sama na Bagadaza, a Iraki.
Ma'aikatar tsaro ta Amurka, Pentagon ta sanar cewa Shugaba Trump ne da kansa ya bayar da umarnin kashe Janar Soleimani, wanda ta ce yana ta kokarin shirya yadda za a kai wa Amurkawa da ke Iraki da kuma yankin baki daya hari.

Hedikwatar tsaron ta kara da cewa harin wani gargadi ne, na duk wani hari da Iran za ta yi tunanin kai wa Amurka. Shugaba Trump ya aika sako na wani katon hoton tutar Amurka a shafinsa na Twitter.

Janar din shi ne babban mai tsara dabaru na Iran a kan Iraki, inda ake kallonsa a matsayin babban mai tsara hare-hare da ayyukan kungiyoyin mayakan sa kai da Iran ke mara wa baya a Syria da Lebanon.
Kasashen Larabawa na daukarsa a matsayin wani shu'umi da ke iya bayyana a ko'ina kuma a ko da yaushe.

Ministan harkokin waje na Iran Javad Zarif ya bayyana kisan Janar Soleimani a matsayin wata tsokana mai hadarin gaske.

Ya ce wajibi ne Amurka ta dandana kudarta kan abin da ya kira kasassabarta.
Wani kakakin Iran ya ce babbar majalisar tsaron kasar za ta yi wani taro domin tattauna abin da ya kira, harin da ke zaman mugun laifi.

Tsohuwar jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley ta ce Qassem Soleimani, babban ''dan ta'adda'' ne da ke da jinin Amurka dumu-dumu a hannunsa, kuma kisansa abin a yaba ne.
Daga 1998, Manjo Janar Qasem Soleimani ya jagoranci dakarun Quds na rundunar juyin juya halin Iran wadda ke aiki a kasashen ketare cikin sirri.

Iran ta yaba da rawar da dakarun Quds suka taka a yakin Syria inda ta zamo mai bayar da shawara ga dakarun Shugaba Bashar al-Assad da kuma dubban masu rike da makami 'yan shi'a da ke mara musu baya.

A kuma Iraki, rundunar ta Quds ta mara wa wasu dakaru na musamman da ke da goyon bayan 'yan shi'a wajen yaki da kungiyar IS.

Tasirin Iran a yankin Gabas ta Tsakiya na karuwa.

Farashin mai ya tashi:

Farashin mai a duniya ya yi tashin gwauron zabi bayan da aka tabbatar da kisan Janar Soleimani.
Farashin man samfurin Brent, ya karu da dala uku a kan ganga, inda ya kai kusan dala 70, lamarin da masu sharhi suka yi gargadin cewa za a iya samun matsalar fitar da mai daga yankin, idan zaman dar-dar ya karu.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

 Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN