Dan Kwakwasiya ne ya kirkiro labarin auren Buhari da Sadiya - DSS

Rahotun Legit Hausa

Hukumar tsaron farin kaya wato DSS a ranar Juma'a ta damke mutumin da ake zargi da kirkiran bidiyon auren karya tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da ministan walwala da jin dadin al'umma, Sadiya Umar Farouq.

Yayinda aka bayyana matashin a hedkwatan hukumar dake Abuja, kakakin DSS, Peter Afunanya, ya bayyana cewa matashin ya amince da kirkiran bidiyon da rabawa kuma dan kungiyar Kwankwasiyya. Peter Afunanya, an kaddamar da bincike ne kan lamarin lokacin da ministar kudi, Zainab Shamsuna, ta shigar da kara.

Yace: "A shekarar 2019, tsakanin watan Agusta da Oktoba, wata bidiyon sharri ta bayyana a fadin Najeriya da ke nuna cewa shugaban kasa na shirin aure da daya daga cikin ministocinsa." "Ta farko itace ministar Ilimi, Hajiya Zainab Ahmad sannan kuma ministar walwala da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Farouq."

"Sunansa Kabiru Mohammed. Dan asalin jihar Kano ne, Yana da shekaru 32. Yayi karatun difloma a ilmin Hausa da Fulfulde a kwalejin ilimin tarayya ta Kano." "Ya tona asirin kansa kuma bincike ya nuna dukkan yadda suka hada bidiyoyin da yadawa."

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN