Allah ya tona asirin wasu mutane bayan yan banga sun kamasu suna mugun aiki

Wasu yan banga a kauyen Manyere da ke kusa da garin Kotonkarfe sun yi nassarar kashe wasu da ake zargi masu sace mutane ne da ke addaban jama'a a babban hanyar Abuja zuwa Lokoja.

ISYAKU.COM ya samo cewa an damke uku daga cikin masu sace mutanen bayan sun yi yunkurin tserewa zuwa cikin daji, kuma daga bisani yan bangan su mika su ga jami'an soji.


An kama bindigu kirar AK47 guda bakwai wanda masu sace mutanen suka yi amfani da su wajen gudanar da aikinsu.

Majiyarmu ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:37 na Asuba ranar Talata 31 ga watan Disamba, lokacin da yan bangan ke sintiri a yankin kafin su ci karo da barayin mutanen.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN