Rahotun Legit Hausa
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanata, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa tsoron abokin tafiyarsa, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da mabiyansa ba tantama za suyi nadama bayan karewar wa'adinsa matsayin gwamna.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani hira da ya gabatar da gidajen rediyon jihar Kano. A cewarsa, gwamnatin jihar Kano a yau na jagorantar al'umma ne bisa ga yaudara da karerayi kuma hakan zai sa gwamnan yayi nadama a karshen wa'adinsa.
"Ko shakka babu za suyi nadama a karshen milkinsu, za suyi da sun sani sun mikawa wanda ya lashe zaben 2019 mulki," Kwankwaso yace. Mun kawo muku rahoton cewa Mai magana da yawun tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran mazhabar Kwankwasiyya,
Hajiya Binta Spikin, ta sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC). Hajiya Sipikin ta sanar da sauya shekarta ne ranar Laraba, daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Wanna ya biyo bayan sauya shekan shugaban jam'iyyar PDP na jihar Kano, Rabiu Sulaiman Bichi, daga PDP zuwa APC.
A jiya, Ganduje ya bayyana cewa Kwankwaso na shirya komawa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) domin tsayawa takarar zaben shugaban kasa a 2023. Ya bayyana hakan ne yayinda ya karba shugaban jam'iyyar PDP na darikar Kwankwasiyya na jihar Kano, Injiniya Rabi'u Sulaiman Bichi wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar
APC. A yayin ziyarar da suka kai gidan gwamnatin jihar, Gwamna Ganduje ya karbesa tare da sauran shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomi 44 na jihar. Yayin bikin karbar Bichi tare da sauran jahororin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, Ganduje ya fada musu cewa "wannan jar hula bata dace daku ba."
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari