Rahotun Legit Hausa
Sakamakon abinda ta kira rashin gamsuwa da tsare tsaren Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, jamiyyar All Progressives Congress (APC) a Akwa ta ce ta janye daga zaben raba gardama da aka shirya yi a ranar Asabar a Akwa Ibom.
Shugaban jamiyya na jihar, Ini Okopido ne ya sanar da hakan yayin taron manema kabarai da ya kira a ranar Juma'a. Okopido ya ce laifin INEC ne shiyasa jam'iyyar ta janye daga zaben. Bayan sanarwarsa wasu yan Najeriya a dandalin sada zumunta sun tofa albarkacin bakinsu a kan lamarin.
Benedict Cool: "Sun barnatar da miliyoyin naira a kotu, yanzu kuma ba su son ayi zaben da suka yi ikirarin cewa su ne suka yi nasara a baya." Usman Kayanta Aduku: "Menene amfanin yin zaben raba gardama idan idan har babban jamiyyar hamayya ta janye daga zaben" Udoma Emmanuel: "Ya kamata a hukunta su. Kada INEC ta wahal da kanta wurin yin zaben domin barnar kudi da kayan aiki kawai za tayi." Uchehi Reuben Ojindu: "Ba a sakin reshe a kama ganye, Akpabio mutum ne mai hikima." Ogumba Ikenna: "Akpabio yana jiran su a kotun koli ko da bai shiga zaben ba. Ku tafi ku tambayi Hope Uzodinmma yadda ya yi nashi.
Haka Najeriya ta ke." Ejigbo Okai: "Akabio ba zai taba sake lashe zabe ko da ta kansila bane a rayuwarsa. Gwamnan su ya gama da shi." Johnson Chinonso Ofoegbu: "Akwai alamun APC ta janye daga zaben ne domin ta tafi kotun koli domin tayi wani siddabaru." Akamo Damilare Dreycool: "Mene yasa suka tafi kotu tun farko. Kawai suna wasa da hankulan mutane."
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari