• Labaran yau


  Duba jarabawa da ya sa wani mutum ke neman taimakon gaggawa a Birnin kebbi

  Sashen jakar Magori na Mujallar ISYAKU.COM, ya samo yadda iyalin wani bawan Allah ke neman fadawa cikin wani yanayi sakamakon yadda mai gidan mai suna Lawali Usman (Taloni) ya sami kanshi cikin jarabawan rashin lafiya mai tsanani.


  Wakilin mu na garin Birnin kebbi ya samo cewa Lawali mazauni unguwar Haliru Abdu a garin Birnin kebbi, ya sha fama ta hanyar jeka ka dawo domin duba rashin lafiyarsa a Asibitin Sarki Sir Yahaya a Birnin kebbi, tare da taimako, agaji da tausayawa na makwabta da abokan arziki kan rashin lafiyarsa. Amma yanzu haka lamarin ci gaba yake yi, sakamakon haka Likitoci suka tura shi Asibitin Tarayya (FMC) da ke Birnin kebbi domin ci gaba ada samun kulawa.,

  Bincike da wakilinmu ya gudanar , ya nuna cewa yanzu haka, iyalin wannan bawan Allah na matukar neman agaji daga bayin Allah , sakamakon yadda gaba daya abin da iyalin suka mallaka ya tafi wajen neman magani., don haka suke neman jama'a su taimaka masu da abin da Allah ya hore.


  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Duba jarabawa da ya sa wani mutum ke neman taimakon gaggawa a Birnin kebbi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama