Yanzunnan: Leah Sharibu ta haifawa wani kwamandan Boko Haram 'da namiji

Rahotun Legit Hausa

Leah Sharibu, yar budurwar da yan Boko Haram suka sace a makarantar Dapchi ta haifi 'da namiji ga daya daga cikin kwamwandojin yan ta'addan. Sahara Reporters ta ruwaito. Leah ta dauki cikin yaron ne tsawon watanni yanzu bayan an tilasta auren daya daga cikin kwamandojin Boko Haram, a cewar majiya mai siqa na kusa da kungiyar.

Majiyan ya ce ta haifi yaron ranar Asabar a kasar Nijar. Majiyan ya kara da cewa bayan Leah Sharibu ta ki barin addininta na Kirista, yan Boko Haram sun tilasta masa karba addinin Musulunci kafin aurar da ita.

Daga baya sun niyyar sakinta, amma ta kasa tafiya saboda tana dauke da juna biyu. Daily Trust ta ruwaito. Leah Sharibu na daya daga cikin dalibai matan da yan Boko Haram suka sace a makarantar gwamnatin Dapchi a watan Febrairu, 2018.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN