Yadda wani suruki ya yi wa amaryar mahaifin matarsa ciki

Rahotun Legit Hausa

Wani tsohon soja mai suna Akwange ya bayyana yadda mijin 'yar shi ya dirkawa amaryar shi ciki. Akwange ya auri amarya Priscilla ne bayan matar shi mai diya mace daya ta rasu. 'Yan uwan shi sun yanke shawarar ya kara aure ne don samun mai kula da Faith. Ma'auratan sun kwashe shekaru 10 bayan auren amma babu haihuwa.

Duk wani asibiti ko wajen maganin gargajiya da za a iya zuwa, Priscilla ta ziyarta, amma shiru ba haihuwa, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito. Daga bisani sai 'yan uwan Akwange suka fara hura mishi wuta a kan ya kori Priscilla don ya auro wata ko zai samu karin 'ya'ya.
Wani tashin hankali shi ke shafe wani don kuwa Faith diyar Akwange ta rasu bayan kwanaki kadan da ta haihu. Tunanin wanda zai rike jaririn ne yasa aka tura Priscilla don zama tare da mijin Faith mai suna Christopher Chori.

Bayan watanni Akwange ya samu wayar abokinsa inda ya sanar masa cewa ya ga Priscilla dauke da katon ciki a kasuwar Lafia da ke jihar Nasarawa. Gani ya kori ji: Hakan ne kuwa yasa Akwange ya wanke kafarsa ya garzaya Lafia. Zuwansa ke da wuya tarar da matarsa da katon ciki. A take ta zube tana rokonsa gafara.
"Ka gafarceni, nasan cikin nan ba naka bane amma ba zan iya zubar dashi ba. Cikin Chori ne kuma shi ya ja hankalina har ya dirka min. Amma kuma na gane cewa ina haihuwa kuma ba zan zubar ba don shekaruna karuwa suke. Ina rokonka da ka rufa min asiri, tare da kareni daga wannan kunyar."

A bangaren Chori kuwa, ya ce matar sirikinsa ce ta ja hankalinsa kuma ya bukaci a zubar da cikin amma ta ki. "Na rasa da idon da zan dubi sirikina don ba yin kaina bane. Matarsa ce ta ja hankalina tare da ra'ayina." Kamar yadda Akwange ya bayyana,

 "Da yanzu ne nake aikin soja, ba shakka zanyi amfani da bindigata don tarwatsa kawunansu. Amma a yanzu dai bana bukatar kara ganinta, zai fi idan ta zauna a wajensa. Shi kuwa na bar shi, alhakina ba zai bar shi ba."

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN