Yadda ta kasance tsakanin Lauyoyin Gwamnati da na Mawakan jihar Kebbi a Kotu

Da misalin karfe goma na safiyar Alhamis, Alkalin babban Kotun Majistare ta 1 da ke garin Birnin kebbi Sama'ila K. Mungadi, ya fara shari'ar da Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Abubakar Bagudu ya shigar a gabanta kan zargin cin zarafin da ya ce wasu Mawakan siyasa na APC a jihar Kebbi sun yi masa a waka da suka rera.

Gwamnan jihar Kebbi ya sami wakilcin babban Lauya na kasa Barista Y.C Maikyau (SAN) wanda ya shiga Kotun tare da tawagarsa ta Lauyoyin Gwamnati da suka hada da Lagalo Dan Lagalo, da Mr.Wasagu wadanda su ne ke kare Gwamanati tare da Gwamnan jihar Kebbi da ya shigar da kara.

A bangaren Mawaka kuwa, akwai Barista A.A Fingilla, Y.A Sani, Mudassir Saleh, da Sani Zagga, haka zalika wasu Lauyoyi da suke kare Mawakan sun hada da Muhammad Nuraddeen, da Nura Bello.

Gaba daya zaman Kotun na yau, ya ta'allaka ne kan muhawwaran Lauyoyi a kan:

1. Ko Kotu za ta iya ci gaba da shari'a ba tare da mai kara ba, watau Sanata Abubakar Atiku Bagudu.
2. Cewa babban Lauya wanda ke wakiltar mai kara Y.C Maikyau SAN, ya yi wa Kotu girma ya a tafiyar da kara a shari'ar bisa matsayinsa na SAN a cikin Kotun Majistare.
3. Cewa Kotu bata da hurumin sauraron shari'ar inji Lauyoyin Mawaka
4. Cewa Y.C Maikyau SAN, Lauya ne mai zaman kansa da ke bukatar gabatar wa Kotu da wata takardar ka'idar shari'a da za ta bashi dama ya gabatar da muhauwaran shari'a a gabanta.
5. Cewa Y.C Maikyau ya bukaci Kotu ta tasa keyar Mawaka uku da aka gabatar a gaban Kotu zuwa Kurkuku kafin a kawo sauran Mawakan guda 15 da basu zo Kotu ba.
6.Cewa Y.C Maikyau ya bukaci Kotu ta daga shari'ar zuwa sati biyu.
7. Lauyoyin Mawaka sun yi muhawwara a kan cewa mako 2 ya yi yawa, sun bukaci Kotu ta sa ranar dawowa a ci gaba da shari'a zuwa mako daya kacal.
8. Lauyoyin Mawakan sun yi kokarin neman Kotu ta bayar da belin Mawakan kafin wannan rana.

Martanin  Kotu:

1.Kotu ta tabbatar da cewa za a iya ci gaba da shari'ar ko da mai kara baya nan a cikin Kotu matukar Lauyansa yana nan, wanda shi ne Y.C Maikyau, tare da tawagar Lauyoyin da ya zo da su domin shari'ar.
2.Cewa Kotu tana da hurumin sauraron shari'ar.
3. Cewa Y.C Maikyau zai iya wakiltan mai kara duk da yake SAN ne matsayinsa a cikin Kotun Majistare.
4. Kotu ta ki bayar da belin Mawakan
5. Kotun ta daga shari'ar zuwa ranar 22 ga watan Janairu 2020.
6. Kotu ta umarci Lauyoyin Mawakan su rubuto bukatar bayar da belin Mawakan a rubuce zuwa gaban kotu, amma ba wai a furucin fatar baki ba sai dai a rubuce.
7. Kotu ta yi umarni a kai Mawakan Kurkuku kafin ranar 22 ga watan Janairu.


Rahotun Musamman daga Isyaku Garba Zuru

Domin tuntuban mu ko shawara  LATSA NAN

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN