Ganyen kuka wanda da ita ake miyar kuka nada matukar amfani ga
lafiyar dan Adam, tana dauke da sinadarai da dama wanda suka hada da
‘Vitamin C’, ‘Vitamin A’, ‘Beta Carotene’, ‘Potassium’, ‘Calcium’ da
saura da dama.
Wadannan Sinadarai kuma na taimakawa wajen magance
wasu matsaloli da cututuka kamar su tari, tsutar ciki, ciwon koda, ciwon
asthma, majinar dake taruwa a kirji da sauransu.
Yara da dama
basu cika son miyar nan ba sakamakon Kasancewar yadda wadansu mata ke
girkawa, Miyar dai nada gwanin dadi idan aka sarrafata da kyau
Abubuwan da za a bukata wajen sarrafa miyar sune:
1 - Kuka
2 - Banddar kifi
3 - Kaza/nama
4 - Citta
5 - Attarugu
6 - Albasa
7 - Magi
8 - Man shanu
9 - Daddawa
10 - Man shanu
Hadi
Da farko Uwar gida za ta wanke Kazarki ko nama yadda ya kamata sannan
ta daura a wuta. Ta yayyanka albasa da tafarnuwa da dan gishiri kadan
sosai, har hadin ya tafasa. Sannan ta dauko kifi banda kamar daya ta
wanke da ruwan zafi sannan ta zuba. Ta jajjaga attarugu hade da daddawa
sai sunyi laushi sannan ta zuba. Ta samu garin citta kadan ta zuba da
magi.
Idan an fara jin kamshin kifi ya bayyana, alama ce cewa
kifin ya nuna sannan a tsame kazar ko namar a ajiye a gefe sannan a debo
garin kuka a rika kadawa kadan-kadan ta yadda ba za ta yi gudaji ba.
Sannan ta rage wuta ya dan sake tafasa kadan. Idan tana bukatar sanya
tokar miya, sai ta zuba kadan ta sake gaurayawa sannan ta sauke.
Wata
miyar kukan Idan aka bar ta a wuta sai ki ga miyan ta tsinke ko ta yi
ruwa, wa ta kuma in taji wuta kauri miyan ya ke yi. Sai a lura
A tuka tuwon dawa ko na masara ko kuma na shinkafa sannan aci da man shanu.
Daga al'ummata
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari