Yadda daliban kwalejin NDA ke cin zarafin matafiya suna tare hanya

Rahotun Legit Hausa

Yan Najeriya kafafaen sadarwar zamani sun bayyana bakin cikinsu gami da damuwar yadda daliban kwalejin horas da hafsoshin Sojin Najeriya, NDA, suke tare manyan hanyoyi tare da muzguna ma matafiya a duk fadin Najeriya. Jaridar Punch ta ruwaito wani bidiyon dake yawo a kafafen sadarwa da jaridar The Herald ta daura ya nuna yadda daliban su biyar sanye da kayan Sojoji suka tare hanya, wanda hakan ya janyo cunkoson ababen hawa a wani babban titi.

Wannan lamari ya zama tamkar al’ada ne ga daliban, inda suke kiransa da Plumming 101, kuma suna yinsa ne a duk lokacin hutun Kirismeti ko sabuwar shekara. A cikin wannan bidiyo an hangi daliban suna rawa a kan titi, suna fareti, sauran kuma suna zagin matafiya dake neman a basu hanya su wuce.

An jiyo daya daga cikin daliban yana cewa: “Babu abin da zasu iya, Ubansu! Babu da zasu iya, dole ne su jira mu, ina take ne, ina take ne? haka nake so, zo mu tafi, wani shegen ne yake danna hon? Kai shege ne? Ubanka!”
A wani bidiyo na biyu kuma an hangi daliban sun tare babban shataletalen Leventis na Kaduna, suka hada cunkoson ababen hawa. Sai dai yan Najeriya da dama sun koka, inda wani mai suna @Fieldaffidavit yace yadda gwamnatin Najeriya ke wulakanta doka ne yasa daliban ma samun yancin cin zarafin yan Najeriya. Shi ma wani @WaleAkinro yace yadda daliban NDA ke wulakanci ya nuna NDA ba ta tsari. @kennygee_70 kuma cewa ya yi:

“Ina fatan rundunar Sojan kasa za ta hukunta daliban nan, Sojojinmu suna da kwarewa, ba kamar yan iskan yaran nan ba dake nuna isa a kan babban hanyar. Daliban yau su ke zama hafsan Soja a gobe.” Sai dai da majiyarmu ta tuntubi mai magana da yawun kwalejin NDA, Manjo Abubakar Abdullahi game da bidiyon, sai yace: ‘Don Allah a bani lokaci, zan mayar da martani.”

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN