Yadda barazanar ruwa ke shafar noman shinkafa ga manoman Fadamar Birnin kebbi

Ruwa da ke fitowa daga Argungu da madatsan ruwa na Goronyo da Bakalori wanda igiyar ruwa ne da ke tafe da karfi, ya jawo wa manoman shinkafa na Fadama da ke Birnin kebbi, Sagaldu, Gabadu, Fakkara, da kuma Indian Water ya jawo rashin yin aikin noma wanda ya shafi manoman shinkafa na rani da damina.

ISYAKU.COM ya samo cewa shugabannin manoma shinkafa a Fadamar Birnin kebbi, sun yi matukar kikari domin tuntubar masu ruwa da tsaki tare da wadanda ya kamata su tuntuba kan lamarin, amma duk da haka ruwan na ci gaba da kwararowa zuwa daruruwan hekta na shinkafa a Fadamar. Wanda haka zai shafi sakamakon samar da shinkafa a wannan Fadama.

Shugabannin, karkashin jagorancin Alhaji Labaran Arab, Aminu VIO, Alh. Aminu Majana, Alh. Abu Majana, Malam Nomau da sauran manoman rani da damana, na daga cikin wadanda suke kokarin ganin an yi abin da ya kamata kan lamarin.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN