Hotunan yadda aka kashe Limami, aka kone Choci tare da gidajen bayin Allah a Kogi

Wasu hotuna maras kyaun gani sun bayyana na yadda aka yi ma wasu bayin Allah kisan gilla a garin Bassa Kwomu da ke jihar Kogi. Rahotanni sun ce wasu yan bindiga ne suka afka wa al'umman garin cikin dare yayin da suke barci. Ana fargaban cewa fiye da mutum 20 ne aka kashe a farmakin.

Kwamishinan yansandan jihar Mr. Ede Ayuba tare da Captain Muhmud sun tabbatar da faruwar lamarin, sun kuma jaddada cewa za a kara wanzar da cikakken tsaro a yankin bayan wannan danyen farmaki.

Shugaban jam'iyar APC na mazaba Ibrahim Simbabi tare da babban Limamin garin na cikin mutum 20 da aka yi wa kissan gilla.

Hakazalika maharan sun kone Mujami'a da gidajen bayin Allah kafin su tsere.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN